Bangladesh

Gobara ta kashe mutane 110 a Dhaka

Dhaka, dake kasar Bangladesh
Dhaka, dake kasar Bangladesh Guillaume Thibault

Mutane 110 suka rasa rayukansu, sakamakon gobarar da ta shi, a wajen wani bikin aure, a Dhaka, dake kasar Bangladesh, yayin da wasu sama da 100 suka samu raunuka.Gobara dai ta tashi ne daren jiya, yayin da ake girkin wani bikin aure, a wani bene, inda wutar tafi karfin mutanen dake wurin, kuma nan da nan ta mamaye gidajen dake wurin, da taimakon iskar gas, dake shake a wasu shaguna, da kuma injin din wutar lantarki.Wani jami’in Yan Sanda, Abul Kalam, yace wutar ta lakume shaguna da dama, tare da gidaje, abinda ya kaiga rasa rayuka, saboda rashin hanyar gudu daga benayen dake Yankin.Jami’in yace, mutane da dama sun yi ta kururuwar neman taimako, amma wutar tayi ta’adi, saboda rashin hanyar da jami’in kashe gobara zasu kai wurin.