Iran

Iran zata kare Yancin ta idan an dora mata sabbin takunkumi

Shugaban kasar Iran, Mahmud Ahmadenajad,
Shugaban kasar Iran, Mahmud Ahmadenajad, Reuters

Shugaban kasar Iran, Mahmud Ahmadenajad, yace kasarsa zata kare Yancin kanta, ko da an sake kakabata sabbin takunkumin Majalisar Dinkin Duniya.Yayin da yake jawabi wajen bikin tuna juyin juya halin kasar da Ayatullah Ruhullah khomeni ya jagoranta, shekaru 21 da suka gabata, shugaban yace suna tsayuwa a fuskan makiya, amma zasu kare kasarsu ta kowanne hali.Ahmadenajad ya kuma soki Amurka da Isra’ila, kan harin da aka kaiwa tawagar jiragen dake dauke da kayan agaji zuwa Yankin Gaza.Yanzu dai haka, kaasr Amurka na kamun kafa wajen wakilan kwamitin Sulhu, na Majalisar Dinkin Duniya, dan ganin an karawa Iran sabbin takunkumi.