G20

Ministocin kungiyar G-20 sun fara taronsu a Busan

G-20
G-20 Reuters

Yau ministocin kudaen kasashe 20 masu karfin tattalin arziki a duniya, wato G-20, sun fara wani taron kwanaki biyu, a Busan, dake kasar Korea ta Kudu, dan nazarin matsalar tattalin arziki, da kuma faduwar darajar kudin Euro.Ministocin za kuma suyi nazarin, kafa wata hukuma da zata sa ido, dan kaucewa fadawa irin matsalar tattalin arzikin da duniya tayi fama da shi, a shekarar 2008 zuwa 2009.Ministan kudin kasar Afrika ta kudu, Trevor Manuel, yace ya zama wajibi su fahimci halin da farfadowar tattalin arzikin yake, kafin taron da za’ayi ranar 26 – 27, na watannan aToronto, dake kasar Canada.