Japan

Sabon shugaban jam'iyyar DPJ mai mulki Naoto Kan ya zama Prime Minista

Naoto Kan sabon Prime Minsiatn kasar Japan
Naoto Kan sabon Prime Minsiatn kasar Japan Reuters / Issei Kato

Jam’iyya mai mulkin kasar Japan, ta DPJ, Democratic Party of Japan, ta zabi Naoto Kan a matsayin sabon shugaba, kuma majalisar dokokin kasar ta tabbatr da shi a mstayin Prime Minista, sanadiyar murubus ta ba zata da Yukio Hatoyama ya yi daga kan mukamun.Mr Kan tsohon Ministan Kudi, ya yi alkawrin kawo sabon tsari wa jam’iyyar ta DPJ da sauye sauye wa kasar. Kuma ya zama sabon Prime Ministan bisa zabin daga majalisar dokokin inda jam’iyyar ta ke da rinjaye. Naoto Kan dan shekaru 63 da hauhuwa, ya zama PM na biyar cikin shekaru uku.PM na kasar ta Japan Yukio Hatoyama, ya bayyana murabus saboda rashin cika alkawarin kawar da sansanin sojan Amurka dake tsirin Okinawa na kudancin kasar.