Bolivia

Wata mata ta saida jariri akan Dala 140

Yan Sanda a kasar Bolivia, sun kama wata mata da ta amsa saida jaririn ta, akan kudi Dala 140, wa wata matar da Allah bai taba bata haihuwa ba.Matar mai suna Jesusa Molle, a karon farko tayi shelar cewa, an sace jaririn ne, a asibitin dake Cochabamba, amma daga bisani, sai tace saida shi tayi.Tuni Yan Sandan suka kama, wanda ake zargi da sayen jaririn, mai suna Suarez.