Argentina

Yan Sanda sun gurfanar da jami’an Gwamnatin sojin kasar

REUTERS/Marcos Brindicci

Yan Sanda a kasar Argentina, sun gurfanar da wasu jami’an Tsohuwar Gwamnatin sojin kasar, wadanda ake zargi da kashe mutane 65.Su dai wadannan jami’ai, ana zarginsu ne da sace mutane, azabtar da su, da kuma kisa, a karkashin Gwamnatin sojin da ta ja ragamar kasar, daga shekarar 1976 zuwa 1983.Kungiyoyin kare Hakkin Bil Adama, na fatar shari’ar zata bada haske, kan yadda jami’an soji ke murkushe Yan adawa.