Afghanistan
Yan Taliban sun kai hari sansanin sojin NATO
Wallafawa ranar:
Yan kungiyar Taliban a kasar Afghanistan, sun kaddamar da hare hare kan sansanin sojin kawancen NATO.Wani jami’in sojin Amurka, yace ba’a samu munanan raunuka ba a harin, wanda shine irinsa na uku, a sansanin sojin saman dake Kandahar, a cikin makwanni biyu.Jami’in yace, Yan Taliban sun harba rokoki hudu, da misalin karfe 3, 8 da kuma 10, agogon kasar.Shi dai wannan sansani na tsakanin birnin Kandahar ne, da kuma sansanin sojin Afghanistan.A wani labari kuma, taron sasanta rikicin kasar da ake gudanarwa yanzu haka, a birnin Kabul, ya bada shawarar tattaunawa da jami’an Taliban, domin samun maslaha wajen warware matsalar kasar.