India
India : hadarin gurbatar mahali
Wallafawa ranar:
Wata kotu a kasar India ,ta yanke hukumcin daurin shekaru 2 kan wasu mutane guda 8 da ke aiki a wani kafanin gaz. Kotun ta samu mutanna ne ,da sakaci na tsawon shekaru 25 ,abun da ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan jama’a. Bayan daurin shekaru 2 za su biyan tara dallar Amurika dubu 2 da dari daya, kudin kasar India Rupees dubu dari. Praministan kasar ta India,Manmohan Singh, ya kwatamta wanan lamari a matsayin wani bala’i da ya kamata a yi kokarin kawar da shi daga cikin al’umma.