UN

Ban Ki Moon ya bukaci Gwanatocin duniya su tashi tsaye wajen kula da lafiyar mata

Ban Ki-moon Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya
Ban Ki-moon Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya © REUTERS

SAKATARE Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon, ya bukaci Gwamnatocin kasashen duniya, da su dauki matakan bunkasa lafiyar mata, dan cimma kudirin Majalisar na rage mace mace.Ban yace, yanzu haka batun kula da lafiyar mata da yara, shine koma baya a cikin kudirorin Majalisar na karni.Sakataren yace, shirinsu shine kowacce mace da yara kanana su anfana da shirin samun lafiya mai sauki.Wani bincike da aka gudanar, ya nuna cewar yayin da ya rage shekaru biyar a kaiga lokacin da aka tsara, kasashe kusan 24 a duniya, suka kama hanyar samun nasara.