Iran

Iran tace babu tattaunawa muddin aka sanya mata sabbin takunkumi

SHUGABAN Kasar Iran, Mahmud Ahmadenajad
SHUGABAN Kasar Iran, Mahmud Ahmadenajad ©Reuters

SHUGABAN Kasar Iran, Mahmud Ahmadenajad, yace zai fice daga duk wani shirin tattaunawa ka shirin nuclear kasar, muddin aka sake kakabawa kasar takunkumi.Shugaban ya baiyana Amurka da kawayen ta a matsayin masu tabka kura kurai, inda yake cewa, maimakon tattauanwa da su, zai gaban kansu suke wajen sanyawa kasar Karin takunkumi.Shugaban ya bukaci kasashen Yammacin duniya, da su amince da yarjejeniyar da Iran tayi da Brazil da Turkiya.Ahmadenajad yace, muddin suka bar wannan dama da subuce musu, to ba za’a sake samun irin ta ba.