Pakistan-US

An Kame Ba’Amurke Mai Farutar Osama Bin Laden A Pakistan

RFI Hausa

A kasar Pakistan an cafke wani Ba’amurke wanda ya yi ikirarin ya fito farautar Osama Bin Laden ne ruwa a jallo.Yayin da aka kama shin an same shi da wata karamar bindiga, gatari da takobi, kamar yadda ‘yan sandsa suka sanar.Mutumin mai shekaru hamsin dan asalin jihar Califonia, yanzu haka ana tsare da shi a tsibirin gundumar Chitral kusa da kan iyakar gundumar Nuristan ta kasar Afganistan, inda ‘yan kungiyar Taliban suka fi kamari.