France

Faransa na shirin kara yawan shekarun ritaya daga aiki zuwa 62

Ministan kwadagon Faransa Eric Woerth
Ministan kwadagon Faransa Eric Woerth Reuters

Kasar Faransa zata kara adadin shekarun da ma’aikaci zai yi ritaya ya kuma sami cikakken fansho, daga shekaru 60 zuwa 62. Sai dai bayan da gwamnati ta sanar da wannan kudiri, kungiyoyin kwadagon kasar sun lashi takobin cewa zasu yaki yunkurin, da ke bukatar sahhalewar majalisar kasar.Ministan kwadagon kasar ya ce ya zama wajibi a kara tsawon shekarun aiki, babu wani siddabaru in ba hakan ba.Minisatan kwadagon Faransan Eric Woerth ya gana da shugaba Nicolas Sarkozy don daukar matsaya ta karshe kan al’amarin, da zai kunshi karin kashi daya cikin dari ga manyan jami’ai, da kuma bullo da manyan hanyoyin samun kudade, don aiwatar da wannan sabon shirin fansho.