Amurka

Obama ya yi rantsuwa sai kamfanin BP ya biya diyyar sakacinsa

Shugaban Amurka Obama yayin da yake jawabi a fadar White House
Shugaban Amurka Obama yayin da yake jawabi a fadar White House Reuters

A karon farko na jawabin da ya yi a ofishinsa na Oval, aka kuma yada ta gidan talabijin, shugaban Amurka Barack Obama ya lashi takobin tilasta wa kamfanin mai na BP sai ya biya diyya, bisa sakacin da ya haddasa kwararar mai a Tekun Mexico. Kiyasin da aka yi na baya-bayan nan ya nuna cewa ita dai wannan kwararar mai kullum tana janyo wa Amurka asarar ganga dubu sittin.Obama ya ce sai an zo taron majalisar zartaswa na Amurkan a fadar White House inda zai umarci shugaban kamfanin Carl-Henric Svanberg lallai ya bude wani asusu don biyan mutanen da abin ya shafa diyya.