Spain

Spain ta amince da shirin dokar yin gyaran fuska ga harkokin kwadago

Prime Minister Jose Luis Rodriguez Zapatero na kasar Spain
Prime Minister Jose Luis Rodriguez Zapatero na kasar Spain Photo: Reuters

A Larabar nan ce majalisar gurguzun kasar Andalus wato Spain ta amince da wani shirin dokar gyaran fuska a harkokin kwadagon kasar, a kokarinta na farfado tattalin arzikinta.Mataimakiyar Firayi Ministan kasar Maria Teresa, wadda ta sanar da hakan, ta ce matakin ya zama wajibi, kuma shi ne mafi muhimmanci irinsa na farko a shekaru ashirin da suka gabata.Wannan mataki da sai majalisar kasar ta amince da shi, zai bai wa ma’aikatu damar sallamar ma’aikata cikin sauki, amma fa har yanzu gwamnati na bukatar goyon bayan ‘yan majalisa bakwai, mafin batun ya sami rinjayen da ake bukata.Manyan kungiyoyin kwadagon kasar biyu CCOO da UGT dake da ma’aikata fiye da miliyan biyu a cikinsu, sun yi kiran a gudanar da yajin aikin gama-gari, ranar 29 ga Satumba, don bijire wa al’amarin.