Amurka

An gurfanar da mutane 10 da ake zargi da leken Asiri wa Russia

FBI Evidence Response Team vehicle
FBI Evidence Response Team vehicle FBI

Mahukuntan kasar Amurka sun caji mutane 10 da ake zargin da leken asiri wa kasar Russia, bayan bincikan aiyukan da suke yi na tsawon lokaci.Wasu daga ciki suna rayu kamar miji da mata, domin batar da kafa, kuma an cafke su bisa shekaru goma da hukumar binciken FBI ta yi akan su.Dukkannin wadanda aka cafke suna rayuwa tamkar sauran al’umma, amma an gano suna da manufar kuste wa harkokin gudanarwar Amurka, tare tara bayanai bisa aiyukan Nuclear kasar, manufofin kasar a Afghanistan da Iran, da kuma dangantaka da Russia.An caji mutanen 10 da laifin hada baki da gwamnatin wata kasa, sannan tara daga ciki an kuma sake cajinsu da laifin halarta kudaden haram.Russia tana jiran Amurka ta bata cikakkun bayanai bisa cafke mutanen da ake zargi da mata leken asiri, kamar yadda Ministan Harkokin Waje Sergei Lavrov. Bayan da bayyana cewa Amurka ta bada labarai masu saba wa juna.