Philippines

Aquino yayi alkawarin yaki da yunwa, cin hanci da rashawa

SABON Shugaban kasar Philippines, Benigno Aquino
SABON Shugaban kasar Philippines, Benigno Aquino Reuters

SABON Shugaban kasar Philippines, Benigno Aquino, yayi alkawarin yaki da talauci, da kuma cin hanci da rashawa. Yayin da yake jawabi bayan rantsuwar kama aiki, sabon shugaban yace, indai babu cin hanci, to babu yadda za’a samu talaka.Sabon shugaban, wanda Da ne wa shugaban kasar da aka kashe, yayi alkawarin magance matsalar sari ka noke da kasar ke fama da shi, da kuma kawo sauye sauye a fannin shari’a.Tsohuwar shugabar kasar, Gloriyo Arroyo, tace bata fargaba kan shirin sabon shugaban na binciken ta.