Amirka

Majalisar Amurka ta amince da zabtare agajin da take baiwa Afghanistan

Nancy Pelosi
Nancy Pelosi (Photo : Reuters)

MAJALISAR Kasar Amurka, ta kada kuri’ar zabtare Dala biliyan hudu, daga agajin da take baiwa kasar Afghanistan, saboda zargin cin hanci da rashawa.Wannan mataki ya biyo bayan zargin cewar, jami’an Gwamnati Afghanistan na ficewa kasar da makudan kudade, dan sharholiya a kasashen waje.Shugabar kwamitin dake bada agaji, Nita Lowey, ta bukaci gudanar da bincike kan yadda Afghanistan ta kashe kudaden da ake bata.