Thailand

Thailand ta kara wa’adin dokar ta baci

GWAMNATIN Kasar Thailand, ta kara wa’adin dokar ta baci da ta sanya a binin Bangkok da wasu Yankuna 19, saboda fargabar tashin hankali.Kakakin Gwamnati, Supachai Jaismut, ya kara da cewa, Gwamnatin ta amince da cire dokar a Yankuna biyar.Kafa dokar ta bacin, ya biyo bayan tashe tashen hankulan da aka samu, tsakanin magoya bayan Tsohon Firayi Minista, Thaksin Sinawatra, da gwamnati mai ci, abinda ya kaiga rasa rayukan mutane da dama.