Faransa

An Daure Tsohon Shugaban Panama Noriega Shekaru 7

Manuel Noriega
Manuel Noriega Reuters

Kotun Faransa yau ta zartas da hukuncin daurin shekaru bakwai gidan yari kan Tsohon Shugaban kama karya na Panama, Manuel Noriega, saboda samun sa da laifin hallata kudaden haram zamaninsa.Kotun ta kuma umarci karbe kaddarorinsa da suka kai na kudin Turai Euro miliyan biyu da dubu dari uku, a bankunan kasar Faransa.Masu shigar da kara sun nemi daure tsohon Shugaban shekaru 10 ne.Wannan tsohon Shugaba, wanda Janar ne na soja nada   shekaru 76.Bayan an kwashe kwanaki 3 ana sauraron kara, a makon jiya, Manuel Noriega ya musanta karban wasu kudaden haram daga hannun dillalan miyagun kwayoyi cikin shekara ta 1980, inda yake zargin kasar Amirka da kulla masa sharri.Lauyan tsohon Shugaban, Yves Leberquier ya fadawa manema labarai jim kadan bayan yanke wannan hukunci cewa, hukuncin yayi tsanani ainun.