Pakistan

Akalla mutane 10 sun hallaka cikin tashin bam

Des milices paramilitaires pendant une opération à Bara, dans la région tribale de Khyber, près de la frontière afghane, le 28 juin 2008.
Des milices paramilitaires pendant une opération à Bara, dans la région tribale de Khyber, près de la frontière afghane, le 28 juin 2008. (Photo : Reuters)

Akalla mutane 10 sun hallaka yayin da wasu masu yawa suka samu raunika, sakamakon tashin bam cikin wata kasuwa mai shake da jama’a, a kasar Pakistan.Jama’ai sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP cewa, lamarin ya faru a lokacin da ake cin kasuwar garin Khyber.Garin yana cikin yankunan kasar ta Pakistan masu cike tsageru masu tada zaune tsaye, kusa da iyakar kasar da Afghanistan.Wani jami’in yankin ya ce wadanda suka hallaka zasu kai 14, sanadiyar tashin wannan bam.Wasu daga cikin kungiyoyin tsagerun yankin sun yi kaurin suna wajen tayar da bama baman dake hallaka mutane.