Iraki

Gobara ta hallaka mutane 29 a wani otel dake kasar Iraki

Reuters

Akalla mutane 29 sun hallaka cikin wata gobara da ta tashi a wani otel dake arewacin kasar Iraki.Wata majiyar asibisti ta shaida wa kamfanin dillacin labaran AFP cewa, akwai akalla ‘yan kasashen ketere bakwai daga cikin wadanda suka hallaka, cikin gabarar na garin Sulaimaniyah.Bakin sun hada da hudu Amurkawa, da wasu inginiyoyi uku, daga kasashe Philippines, Sri Lanka da Cambodia, suna cikin wadanda su hallaka, yayin tashin wutar cikin dare Alhamis. Kamar yadda shugaban kamfanin da suke ziyarar aiki na sadarwa ya tabbatar.Akwai yara hudu cikin wadanda suka rasa ransu, yayin lamarin na garin Sulaimaniyah dake yankin Kurdawa mai arzikin man fetur.Jami’ai suna zargin cewa wayoyin wutar lantarki suka haddasa hadarin.