Guinea Conakry

Kasar Guinee maganar tsaro kan zaben kasar

La Haute-Guinée est un fief d'Alpha Condé. Dans ce village, le portrait du leader a été peint sur le bureau local du RPG, le Rassemblement du Peuple de Guinée .
La Haute-Guinée est un fief d'Alpha Condé. Dans ce village, le portrait du leader a été peint sur le bureau local du RPG, le Rassemblement du Peuple de Guinée .

Jami’an tsaron a kasar Guinee Conakry, sun bankado wani shirin kawo tashin hankali da wasu ke kokarin yi, a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu. Praminista kasar Jean-Marie Dore ,ya ce an cafke wadanda ake zargin da neman kawo hargitsi ga shirin da kasar ke yi na madda mulki ga hunnun farar hula.Ya ce ,mutanen sun nemi kayen sarki irin na jami’an tsaro da nufin yin shigar burtu. Babban habsan sojan kasar Kanal Nouhou Thiam ya tabbatar da labarin.Shugaban kasar ta Guinee Conakry Janar Sekouba Konate ya yi alkawarin maida kasar bisa tafarkin demokaradiya, inda ake shirin gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu.