Amirka-Britaniya

Shugaba Obama Ya Gana Da PM Cameron

Shugaban Amirka da PM Britaniya
Shugaban Amirka da PM Britaniya rfi

Shugaban kasar Amirka Barack Obama yayi marhabin da Prim Ministan  kasar Britaniya David Cameron, a wani ziyara da itace ta farko da Prim Ministan ya kai Washington na kasar Amirka.Fadar Shugaba Amirkan ta karrama prim Ministan da kuma matar sa inda suka ci abincin rana da kuma basu wasu kyautuka daga mai masaukin nasa Barack Obama.Shugabannin biyu sun tabo batun sakin dan kasar Libyan nan da ake zargi da kai harin bam wani jirgin sama a Lockerbie, da al’amarin burmewar bututun mai karkashin tekun gaban ruwan Mexico da kuma lamarin aikin da dakarun Amirka dana kawayenta keyi akasar Afghanistan.Shugabannin biyu sun bayyana burin su na ganin sun warware dukkan matsala ta tattaunawa da juna.Shugaba Obama ya bayyana gamsuwa da tattaunawan da sukayi.Prim Minista Cameron yayi amfani da daman inda ya kare kamfanin mai na BP da ake zargi da sakaci har bututun sa ya fashe.