FARANSA

‘Yan sanda sun tarwatsa masu neman toshe matatun Mai

'Yan sandan kasar Faransa
'Yan sandan kasar Faransa

Bayan da Gwamnatin kasar Faransa ta bada umurni ga ma’aikata su janye yajin aiki su koma ga aikinsu, a yau juma’a ‘Yan sandan kasar sun tarwatsa gungun masu gudanar da yajin aiki dake neman shiga matatar man petir dake samar da mai ga yankin Paris.Watanni biyu ke nan da ma’aikata ke gudanar da yajin aiki kan yaki da shirin shugaban kasar Nicolas Sarkozy na Karin wa’adin shekarun ritaya daga shekaru 60 zuwa 62.Yajin aikin dai ya kawo cikas ga matatun man kasar guda goma sha biyu, kuma a yau jum’a kusan gidajen mai da dama ne, man petir ya katse masu sanadiyar yajin aikin, kamar yadda ministan muhalli da Sufuri Jean-Louis Borloo ya shaidawa manema labarai.A yau juma’a ne kuma a ke sa ran majalisar dokokin kasar zasu amince da shirin na shugaba Sarkozy