Namibiya - Jamus

An kama wani abu da ake zargin bom ne a Jirgin Jamus

Taswirar kasar Namibia
Taswirar kasar Namibia Wikimedia commons

Jami’an tsaro a kasar Nimibia sun kama wani abu dunkule da ake zargin bom ne lokacin da ake lodin kayan wani jirgin yawon bude ido na kasar Jamus a filin saukar jiragen Windhork a kasar.Mahukuntan filin saukar jirgin sun bayyana cewa a daidai lokacin da Jami’an tsaro ke gudanar da bincike na tantance kayan matafiyan ne aka samu wani abu da aka dunkule da takarda cikin kayan daya daga cikin fasinjojin jirgin, kodayake har yanzu ba a tantance al’amarin ba.A wani bayani da hukumar kula da filayen jiragen kasar Nimibia ta fitar, hukumar ta bayyana cewa jirgin wanda zai nufi Munich ba zai tashi ba har sai an kammala bincike.