Lebanon

Hezbollah ta bukaci Lebanon ta fice daga Kotun MDD

Hassan Nasrallah shugaban kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon
Hassan Nasrallah shugaban kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon Reuters / Issam Kobeisy

Shugaban Kungiyar Hezbollah, Hassan Nasrallah, ya bukaci gwamnatin kasar Lebanon da ta janye a kotun Majalisar Dinkin Duniya, dangane da shari’ar kashe Tsohon Prime Minista, Rafiq Hariri.Nasrallah ya shaida wa taron dubban magoya bayansa cewa, rana tana zuwa inda asirin duk wadanda suka hada kai da kotun zai budu, kamar yadda dandalin Wikileaks ke tona asiri yanzu.