Amurka-Turai

Turai da Amurka sun bayyana shirin karfafa zaman lafiya Gabas ta Tsakiya

Catherine Ashton babbar jami'ar harkokin wajen Tarayyar Turai
Catherine Ashton babbar jami'ar harkokin wajen Tarayyar Turai © REUTERS

Kungiyar kasashen Tarayyar Turai da kasar Amurka sun bayyana matukar aniyarsu na samar da kasar Palastinawa mai cin gashin kanta a gefen kasar Izra'ela, ba tare da shata wani wa’adin faruwar hakan ba.A lokacin wata ganawa da ta yi da manzon musaman na kasar Amurka kan yankin gabas ta tsakkiya George Mitchel, a birnin Bruxelles na kasar Belgium, shugabar sashen diplomasiyar kungiyar ta tarayyar Turai uwargida Catherine Ashton, ta bayyana cewa, kungiyar ta tarayar Turai da kasar Amurka, zasu yi aiki tukuru wajen ganin an samar da cikakkiyar kasar Palastinu.