Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta yi tir da harin da aka kai kudancin Sudan

Shugaban kasar Sudan Hassan Umar Albashir
Shugaban kasar Sudan Hassan Umar Albashir Reuters
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
Minti 2

Fadar White house ta Amurka ta yi Allah waddai da harin da dakarun soji suka kai wa fararen hula a yankin Darfur dake kudancin Sudan kafin fara zaben raba gardama da za’ a gudanar a kan kudancin kasarA cewar Mike Hammer mai Magana da yawun kwamitin tsaro a fadar White house, ya bayyana cewa Shugabannin kasar Sudan hakkin su ne wajen kare rayukan fararen hula a kasar. Mista Hammer ya kara da cewa Kasar Amurka ta damu matuka kan rehotannin harin da Sojin kasar suka kai wa wani kauyen Khor Abeche dake kudancin Darfur.A karshen makon daya gabata ne Sojojin kasar Sudan suka kai farmaki a Khor Abece dake da nisan kilomita 80 tsakaninsa da Darfur babban birnin kasar inda mutane sama da mutane 250 a kauyen suka gudu don neman mafaka a wasu wurare bayan kone gidajensu.A yanzu haka dai shuwagabannin kudancin Sudan sun zargin Shugaba Umar Hassan Al Bashir da Jam’iyyarsa a kokarin kulla wata makarkashiyar wargaza zaben raba gardama tsakanin yankunan kasar guda biyu. 

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.