Amirka

Sanhi ya hadasa matsalar suhuri a Amurika

Wani hilin jirgin kasar AMURIKA
Wani hilin jirgin kasar AMURIKA Reuters / Yuri Gripas

Matsalar sanyi da zubar dusar kankara, sun kawo cikas ta bangaren lamuren zirga- zirga a gabastin Amurika.Lamarin ya sa an soke sauka da tashin jirage sama 1400 tare da sufurin motoci da jiragen kasa. Rahotanni sun ce, an rufe tashar jiragen saman birnin New York, yayin da kanfanin jiragen kasar Amtrak, ya katse zirga- zirgar shi tsakanin garin New York da na Boston.Lamarin ya jefa dubban matafiya cikin halin kaka-ni-ka-yi.