Cuba

Castro ya soki Amurka, da Ingila da kuma Isra’ila bisa kisan masana kimiyyar Iran

©Reuters

Juma’ar nan Fidel Castro na Cuba ya yi tofin Allah tsine kan Amurka, da Birtaniya, da kuma Isra’ila, wadanda ya ce suna ta faman yi wa masana kimiyyar kasar Iran kisan gilla, don gurgunta shirin Tehran na Nukiliya.Castro mai shekaru 84 ya dogara da rahotannin kafafen yada labaran duniya, wajen kafa hujjar zarginsa na cewa, hukumomin tsaron kasashen uku ne ummul-aba’isin bacewar masana kimiyyar Nukiliyan kasar Iran.Cikin wata makala da ya rubuta aka kuma buga a wata jaridar kasar, Castro ya ce akwai karin hujjojin dake yin ishara ga yadda kasashen na yamma ke ta faman kashe masana kimiyyar Iran irinsu Massoud Ali Mohammadi tun daga shekara ta 2007.