Gaza

Alliot-Marie ta gamu da fushin al’ummar Gaza

Gungun masu zanga zanga lokacin Michele Alliot-Marie  ke kokarin kai ziyara birnin gaza
Gungun masu zanga zanga lokacin Michele Alliot-Marie ke kokarin kai ziyara birnin gaza AFP/Mahmud Hams

Gungun Palasdinawa ne suka rufarma ministan harakokin wajen Faransa Michele Alliot-Marie lokacin da ta ke kokarin kai ziyara birnin Gaza a yau Juma’a. Lokacin da minister ta isa Gaza, tawagarta ta ci karo da gungun masu adawa da ziyarar kuma ziyararta ta farko tun bayan kaddamar da ita ministar harakokin waje a watan Nuwamba. A lokacin ne dai ta kai ziyara babbar asibiti dake birnin na Gaza.Lokacin da take jawabi Michele Alliot-Marie ta yi kwakkwaran kira wajen ganin kawo karshen rikici tsakanin Isra’ilawa da al’ummar Palasdinawa.Tun wayewar safiyar yau ne gungun masu zanga zangar suka rufe hanyoyin shiga birnin na gaza dauke da sakon da ke cewa “ku fice daga Gaza”. Al’amarin da har ya kai wasu daga cikinsu suka farma motar da Ministar ke ciki kan kalubalantarta dangane da wasu munanan kalamai da aka alakanta ministar dasu lokacin da ta ke ganawa da iyayen sojan Isra’ila Gilad shalit a Jarusalem wanda kungiyar Hamas tayi karkuwa da shi.A lokacin ne dai kafar yada labaran Isra’ila da harshen larabci ta yada labarin cewa Michele Alliot-Marie ta bayyana cewa ya zama dole kungiyar Tarayyar Turai ta yi Allah waddai da ta’addancin da Hamas ke aikatawa na garkuwa da Gilad Shalit.Lokacin da take jawabi da manema labarai, ministar tace sama da mutane hamsin ne suka kewaye motarta, kuma cikin masu zanga zangar sun hada da mata da kananan yara. Ministar tace ‘yan sandan Hamas ne suka kwace ta hannun masu gudanar da zanga zangar tare da tarwatsa su don samar mata hanyarta ta zuwa birnin Gaza.