Japan

Ministan Harkokin Wajen Japan Maehara ya ajiye aikin

Ministan Harkokin Wajen Japan, Seiji Maehara, ya ajiye aikinsa, saboda sukar da aka masa, na karbar taimakon kudin Yen 50,000 daga wajen wani Dan kasar Korea ta Kudu.Dokokin kasar sun hana karbar taimako daga kasar waje, abinda ya sa 'yan adawa suka bukace shi da ya sauka daga mukamin. Tuni Prime Ministan kasar ta Japan Naoto Kan ya yi watsi da kirar neman ya sauka daga mukamusa, bayan wannan murabus na ministan harkokin waje cikin karshen mako.Kan ya shaida wa majalisar dokokin kasa cewa zai ci gaba da rike mukamunsa zuwa zabukan kasa baki daya a karshen shekara ta 2013. Yan adawa keda rinjaye a majalisar dattawa.

Seiji Maehara ministan harkokin Japan da ya yi murabus
Seiji Maehara ministan harkokin Japan da ya yi murabus Reuters