Palasdinawa-Isra’ila
Sabon shirin neman zaman lafiya na Gabas ta Tsakiya
Wallafawa ranar:
Shugaban Palasdinawa, Mahmud Abbas, ya isa Birtaniya, dan gudanar da taro, kan yadda za’a farfado da tattaunawar samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.Ana saran yau shugaba Abbas zai gana da Prime Minista, David Cameron, da Ministan harkokin waje, William Hague. Wannan yana cikin shirin neman samar da zaman lafiya wa yankin da kasashen duniya ke ci gaba.