Colombiya

Ana garkuwa da ma'aikatar kamfanin mai 23 a Colombia

Bogotá babban birnin kasar Colombia
Bogotá babban birnin kasar Colombia ©Reuters

Kamfanin hakar man fetur na Talisman Energy dake kasar Canada, ya ce an sace masa ma’aikata 23 a kasar Colombiya.Kakakin kanfanin, Tomas Reuda, ya ce ma’akatan da ake garkuwa da su, duk 'yan kasar ta Colombia ne, wadanda wasu 'yan bindiga da ake zargin Yan kungiyar 'yan tawaye masu ra'ayin makisanci, FARC, su kayi awon gaba da su. Kasar ta Colombiya ta shafe shekaru masu yawa tana fuskan tashe tashen hankula na garkuwa da mutane daga 'yan tawayen na kungiyar FARC, ko da yake gwamnatin kasar da dauki tsauraran matakan shawo kan lamarin.