Brazil

An kama masu fitsari kan tituna a Brazil

Shugaban Brazil Rousseff
Shugaban Brazil Rousseff © REUTERS

Hukumomin birnin Rio de Janeiro, dake kasar Brazil, sun ce mutane 214 suka kama a karshen mako wajen kamala bikin Carnival da akayi, saboda laifin fitsari akan tituna.Alex Costa, jami’in kula da tsabtace birnin, wanda aka baiwa damar daukar nauyin gasar Olympics na shekarar 2016, yace zasu cigaba da kama masu fitsari a titi, saboda rashin mutunci ne ga birnin, da kuma mutanen sa.