Amurka

Shugaban Amurka Obama na tunkarar maganar 'yan fursunan yaki

Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama Reuters/Jason Reed

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama, ya sanar dage dokar shari’ar wadanda ake tsare da su a gidan yarin Guantanamo Bay.Shugaban ya kuma sanar da sabbin hanyoyin tsare wadanda ba a fara musu shari’a ba, ko kuma wadanda ba a daure ba, amma ana ganin sake sun a da hadari.A wani yanayi da ake ganin kamara shugaban ya yi amai ya tande, shugaba Obama wanda ya yi alkawarin rufe gidan yarin na Guantaamo da zaran ya hau karagar mulki, ya bada dokar kula da wadanda ba a same su da laifi ba, kuma ana ganin sakinsu yana da hadari.A wata sanarwa da yayi, shugaban yace matakin ya biyo bayan kudirinsu na ganin duk an hukunta masu aikata laifufuka, inda ya bukaci Sakataren Tsaro Robert Gates, da ya janye umurnin farko, wanda ya bayar lokacin da ya karbi ragamar mulki.Shugaban dai ya sha suka daga 'yan Jam’iyyar adawa ta Republican, dangane da shari’ar wadanda ake zargi da aiyukan ta’adanci a kotun gama gari, abinda Gwamnatin shugaba Bush taki a baya.Tuni manyan 'yan majalisar dattawar kasar, suka yaba da sabon matakin, cikinsu harda Dan Majalisa Peter King.