Faransa

France:Yan sanda sun bincike cibiyar jama’iyar UMP ta shugaban kasar

Cibiyar jama'iyar  UMP ta Nicolas Sarkozy a birnin  Paris
Cibiyar jama'iyar UMP ta Nicolas Sarkozy a birnin Paris AFP/Patrick Kovarik

Yan Sanda a kasar Faransa, sun gudanar da bincike a ofishin Jam’iyar UMP ta shugaba Nicolas Sarkozy, saboda zargin da ake na karban kudade ba bisa ka’ida ba.Kudin da ake ganin an karbo su daga hannuwan attajirar nan Lilliane Btancourt.Ana zargin Ministan aiyuka, Eric Woerth, da karbar makudan kudaden tallafi daga attaijirar, da kuma taimaka mata wajen kaucewa biyan haraji.