Hukumomin kasar Saudia sun karfafa tsaro
Yan sandan kasar Saudiya, sun bude wuta ga wasu mutane masu zanga-zanga da yawan su ya kai 600 zuwa 800, da kuma su ka kassance maza da mata 'yan shiya. Rahotanin na cewa akalla mutane 3 sun samu ranika a lokacin da ‘yan sandan suka buda wuta ga masu zanga-zangar a garin Al’Qateef.Yau Jumma'a hukumomin kasar sun karfafa matakan tsaro, bayan kiranye kiranye da shafukan yanan gizo na neman zanga zanga, domin ganin an kaddamar da sauye sauye siyasa da suka hada da kafa majalisar dokokin wadda mutane zasu zaba, da kara sakin mara wa 'yan kasa.Akwai kasdashen Laraba masu yawa dake fuskan wannan zanga zangar, kuma masu shiryawa suna da karfin gwiwa, bayan kifar da gwamnatocin kasashen Tunisiya, Masar da kuma rincabewar lamuru a kasar Libya.
Wallafawa ranar: