Kasashen Larabawa

Kasashen Larabawa sun amince da hana sufuri sama a Libya

Kasashen Larabawan yankin Golf da kasar Saudiya ke jagoranta sun sake jadda goyan bayansu ga shirin saka takunkumin kan sararin samaniyar kasar Libiya, tare da jaddada bukatar ganin kungiyar kasashen larabawa ta Ligue Arab, ta bada tata gudunmuwa domin tabbatar da nasarar yin hakan.Kasashen 6 na yankin Golf da suka gudanar da zaman taronsu a marecen jiya alhamis a birnin Ryad na kasar Saudiya Arabiya, sun danganta gwamnatin Kaddafi da zama haramtaciya, tare da neman takwarorinsu na kasashen larabawa da gobe Assabar zasu gudanar da zaman taronsu a birnin Cairo na kasar Masar, da su dauki nauyin da ya rataya a wuyansu, wajen dakatar da zubar da jinin da ake yi a kasar ta Libiya. 

Photo RFI : Donaig Le Du et Manu Pochez