Bahrain

Dakarun Saudiya sun shiga Bahrain

Yan tawayen kasar Bahren sun bayyana cewa, kasancewar dakarun kasashen waje a cikin kasar, zai zama tamkar mamayen kasar ne, wannan kuma yana kasancewa ne a matsayin mayar da martani kan labarin dake nuna cewa, dakarun kasar Saudiya sun shigo kasar, domin taimakawa murkushe zanga zangar da masu kin jinin gwamnatin kasar ta Bahrein ke yi.Yan adawar sun bayyana cewa, sun samu kishin kishin cewa dakarun kasar Saudiya sun shigo kasar ta Bahrain ne, a ranar jiya Lahadi, wanda suka danganta a matsayin mamayen da ya sabawa ka’ida.  

Reuters