Rasha-Turai

Rasha da kasashen Turai na sake duba aiyukan Nukilya

Reuters

Prime Minsitan kasar Rasha Vladimir Putn ya buka sake duba aiyukan Nukiyar kasar, bayan girgizar kasa data dagula aiyukan nukiyar kasar Japan.Sauran gwamnatoci kasashe cikin nahiyar Turai na ci gaba da sake duba aiyukan nukiyar, bayan fashe fashen da aka samu a tashoshin nukiyar Japan, sanadiyar girgizar kasa da Tsunami da suka afka wa kasar.Tuni kasashen Jamus da Switzerland suka jingine aiyukan nukiyarsu, yayin da ministoci da masana na nahiyar ta Turai ke gudanar da taro, domin duba hanyoyin shawo kan matsalolin da ka iya tasowa.