UN

Majalisar Dunkin Duniya ta amince da matakin Soji kan Libya

kwamitin Tsaro na Majalisar Dunkin Duniya lokacin da yake ganawa kan rikicin Libya
kwamitin Tsaro na Majalisar Dunkin Duniya lokacin da yake ganawa kan rikicin Libya REUTERS/Jessica Rinaldi

Majalisar Dunikin Duniya ta amince kan daukar matakin soji ga shugaban Libya Muammar Gaddafi tare da daukar matakin kare fararen hula, sai dai kuma dakarun shugaba Gaddafi suna gab da kai farmaki ga ‘yan tawayen kasar tare da ikirarin tarwatsa su.Wata majiya daga ofishin jekadancin Faransa ta bayyana cewa za’a kaddamar da matakin cikin gaggawa wanda kuma ya hada kasashen Faransa da Birtaniya da Amurka da kuma wasu kasashen larabawa.Lokacin da yake jawabi a kafar yada labaran Telebijin ta Al Arabiya, Saif Islam ya bayyana cewa basu da wata fargaba ga matakin da Majalisar Dunkin Duniya ke kokarin dauka kan Libya kuma a shirye suke su kare kansu.Lokacin da shugaba Gaddafi ke jawabi a radion kasar dangane da Benghazi, shugaban yace zasu bi gida-gida, daki-daki domin fatattakar ‘yan adawa.A taron gaggawa na kwamitin tsaro na Majalisar Dunkin Dunkin Duniya, kwamitin ya amince da kakubawa Libya takunkumin shawagin jiragen sama a sararin samaniya. Ana dai tunanin kungiyar NATO zata taka muhimmiyar rawa ga matakin kwamitin. sai dai kuma kasar Rasha da kasar Sin da ke da karfin Fada a aji a kwamitin tsaro na Majalisar Dunkin Duniya sun nisanta kansu da wannan matakain da kwamitin ya dauka kan kasar Libya.