Yemen

An kafa dokar ta baci bayan mutuwan mutane 45 a kasar Yemen

Reuters/Khaled Abdullah

Wasu bindiga dadi sun bude wuta wa masu zanga zangar kasar Yemen baunda ya janyo mutuwar akalla mutane 45, yayin da wasu kusan 300 suka samu raunika.Tuni shugaban kasar Ali Abdullah Saleh da ake bore neman ya yi murabus bayan mulkin shekaru 32, ya aiyana dokar ta baci tare da cewa dakarun kasar basu da hanu cikin harin, wanda akakai Sana’a babban birnin kasar.