Amurka
Shugaban Amurka Obama ya fara ziyara kasashen Latin Amurka
Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya fara ziyarar aiki ta kwana biyar a kasashen Latin Amurka, da nufin fadada kasuwannin kasar.Obama zai fara yada zango a kasar Brazil wadda ta zama babbar kasuwar Amurka a yankin, inda zai gana da sabuwar shugabar kasar Dilma Rousseff.Daga bisani shugaban na Amurka Barack Obama zai kai ziyara kasashen Chile da El Salvador.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar: