Haiti

Tsohon shugaban kasar Haiti Aristide ya koma gida

Jean-Bertrand Aristide Tsohom Shugaban kasar Haiti
Jean-Bertrand Aristide Tsohom Shugaban kasar Haiti REUTERS/Shannon Stapleton

Tsohon shugaban kasar Haiti Jean-Bertrand Aristide ya koma gida, inda ya sauka a Port-au-Prince babban birnin kasar, bayan gudun hijira na shekaru bakwai a kasar Afrika ta Kudu.Ya isa kwanaki biyu kafin zaben shugaban kasa zagaye na biyu.Mr Aristide wanda tawayen shekara ta 2004 ya tilasta masa ban kwana da madafun iko, ya bayyana ficewa daga cikin harkokin siyasar kasar ta Haiti.