Haiti

Ana zaben shugaban kasa zagaye na biyu a Haiti

Reuters

Yau Lahadi al’umar kasar Haiti ke gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu, domin tantance wanda zai jagoranci kasar na gaba.Ana fafata zaben tsakanin Michel Martelly da matar tsohon shugaban kasar Mirlande Manigat, kuma duk wanda ya samu nasara nada aikin sake gina kasar da girgizar kasa da chutar amai da gudawa suka yi wa kasar kaca kaca.Zaben na kasar ta Haiti ya zo daidai lokacin da tsohon shugaban kasar Jean-Bertrand Aristide ya koma gida daga gudun hijiran shekaru bakwai a kasar Afrika ta Kudu.