Siriya

Jami'an Tsaron Siriya sun tarwatsa masu zana'ida

AFPTV

Jami’an tsaron kasar Siriya sun yi anfani da hayaki mai saka hawaye kan masu zana’idar mutane biyu da suka hallaka, yayin zanga zangar nuna kiyayya wa gwamantin kasar.Dubban mutane sun hallara a wajen zana’idar, wadda akayi a garin Deraa na kundancin kasar, idan aka rera wakokin rashin amincewa da gwamnati.Shugaban kasar ta Siriya Bashar Al-Assad ya gaji kujerar mulki daga mahaifinsa a shekara ta 2000, kuma jam’iyyar Baath ta kwashe shekaru 50, sai yadda ta yi da harkokin siyasar kasar, kafin wannan juyin juya hali ya fara mata barazana.