Yemen

Wasu jiga jigan jam'iyya mai mulkin Yemen sun yi Murabus

Reuters/Khaled Abdullah

Manyan jiga jigan jam'iyya mai mulkin kasar Yemen biyu sun yi murabus, domin nuna rahsin jin dadi kan yadda aka hallaka masu zanga zangar nuna kiyayya wa gwamnatin kasar.Wannan daidai lokacin da masu zanga zangar neman shugaba Ali Abdullah Saleh ya yi murabus bayan mulkin shekaru 32, suka ce babu gudu babu ja da bayan wajen ci gaba zanga zanga har sai shuga Saleh ya yiban kwana da madafun iko.