Siriya

Jami'an Tsaron Siriya sun hallaka Mutane biyar masu zanga zanga

REUTERS/Khaled al-Hariri

Jami'an Tsaro a kasar Siriya, sun bude wuta kan masu zanga zanga kusa da wani Massalachi a birnin Daraa, inda suka kashe mutane biyar.Daruruwan mutane ne suka taru a Massalachi, wanda ya zama matattarar masu zanga zangar, dan hana Yan Sanda kusa kai ciki, abinda ya sanya su bude wuta.Kasar Faransa ta nemi gwamnatin kasar Siriya da ta fasa amfanin da karfi da take yi kan masu zanga zanga a kasar, tare da yin tir da tashe tashen hankulan da suka yi sanadiyar mutuwa tare da jikkata mutane da dama a cikin daren jiya kawo safiyar yau laraba a birnin Derra’a.Faransa ta sanar da haka ne a yau Laraba, a cikin wata sanarwa da ma’aikatar harakokin wajenta ta fitar.