Shugaban Yemen Saleh ya yi gargadin kan nema kawar da shi daga Mulki
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugaban kasar Yemen Ali Abdullah Saleh ya yi gargadin cewa yunkurin kawar da shi daga kan madafun ikon kasar da karfi, zai jefa kasar cikin yakin basasa.Ya soki abun da ya kira neman kifar da gwamnati ta hanyar juyin mulki, wanda ya ce ba zata yuwu ba.Tuni manyan habsoshin sojan kasar suka bayyana goyon baya wa masu zanga zanga, bayan kwashe makaonni ana zanga zangar neman shugaba Saleh, ya ajiye aiki bayan mulkin shekaru 32, a kasar ta Yemen mai fama da matsaloli.Manazarta na ganin cewa ta faru ta kare wa shugaba Abdullah Saleh, wanda ke rasa ta cewa ko wani wayewar gari.Fiye da mutane 50 sun hallaka, yayin da wasu daruruwasuka samu raunika, sakamakon rikicin siyasar kasar ta Yemen, inda masu zanga zanga ke neman ganin bayan gwamnatin Saleh.Yan adawa a kasar ta Yemen, sun yi watsi da dokar da 'yan majalisar dokokin kasar suka rattabawa hannu, wace ta amince da kafa dokar ta baci a kasar, dake fama da tashe tashen hankullan zanga zangar al’umma, kamar yadda wani dan majalisar jam’iyar adawa mai ra’ayin Isalama Abdel Razak Al Hejri ya sanar.Dan majalisar ya bayyana zaben da 'yan majalisar suka yi, da cewa haramtace ne, domin kuwa 'yan majalisu 133 ne kawai, daga cikin su 301 da ake dasu a majalisar suka halarci zaben.